fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Allah yayi wa matar mai martaba Sarkin Jama’a rasuwa

Mai martaba sarkin Jama’a a jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya rasa matarsa ​​ta hudu, Hajiya Zainab Muhammad Isa.

Sakataren Majalisar Masarautar Jama’a, Alhaji Yakubu Isa Muhammad (Dokajen Jama’a) ne ya sanar da wannan labarin a ranar Litinin 13 ga Satumba.

Tuni aka yi jana’izar marigayiya Hajiya Zainab Muhammad kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a Kafanchan, hedikwatar Karamar Hukumar Jama’a.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *