fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Allah Yayiwa Walin Kontagora ta jihar Neja Rasuwa

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya nuna alhininsa kan rasuwar Walin Kontagora, Muazu Wali.
Wali ya yi aiki a matsayin shugaban dakin karatu na kasa, Abuja.
Shi ne mijin Babbar Sakatariya a gidan Gwamnatin Jihar Neja, Hauwa Isah Wali.
A cikin sanarwar, Gwamnan ya yi ta’aziyya tare da Sarkin Sudan da dukkan masarautar Kontagora.
Bello ya bayyana Wali a matsayin fitaccen ma’aikacin gwamnati wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga bautar kasa da bil’adama.
Gwamnan ya roki Allah da ya gafarta masa kurakuransa kuma ya saka masa da Aljannatu Firdaus.
“Allah yana bayarwa kuma yana daukar rai a lokacin da ya ga dama, ina kira ga dangi da abokan arziki da su yarda da nufinsa”, in ji shi.
Marigayin an haife shi ne a watan Disambar 1940, ya mutu ne a ranar Juma’a bayan rashin lafiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *