fbpx
Monday, September 27
Shadow

‘Allah zai sake ba wa ƴan Najeriya shugaba irin Buhari’

Gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi ya yi addu’ar Allah ya sake ba wa ƴan ƙasar shugaba mai kyakkyawar zuciya da kishin kasa kamar shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen 2023.

Jaridar The Punch ta rawaito gwamnan na jinjina wa shugaban ƙasar kan wasu manyan ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ta samar a yankin kudu maso gabashin Najeriya tun bayan hawansa mulki a 2015.

Yana magana ne jim kadan bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban ƙasa a Abuja, inda yace ya je ne domin mika masa godiya ta musamman saboda yadda yake daukar yankin da muhimmanci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *