fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Amfani da karfin Bindiga kadai ba zai magance matsalar tsaro a Najeriya ba >>Hukumar Sojojin Najeriya

Hukumar Sojoji Najeriya a jiya, Laraba ta bayyana cewa, Bindiga kadai ba zata yi maganin matsalar tsaro a Najeriya ba.

 

Kakakin Sojojin Najeriya,  Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka a Abuja inda yace matsalar na bukatar a tunkareta ta bangarori daban-daban.

 

Ya bayyana hakane a jawabinsa wajan kama aikin me magana da yawun soji daga hannun tsohon me rike da mukamin, janar Muhammad Yerima.

 

Yace dolene a hada hannu da masu ruwa da tsaki a harkar, misalin kafafen yada labarai dan shawo kan matsalar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *