fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Amfanin Al’basa ga jikin Dan Adam da yadda ake sarrafata domin magance zubar gashi da sauransu

Tana Yaki Da Cutar Daji (Kansa) Sakamakon da aka samu daga binciken da aka yi, ya nuna cewar,albasa ta kasu daban daban, idan ana mafani da ita akai akai, tana rage yiyuwar kamuwa da cutar kansa, kamar kansa ta colorecta, oral kansa, kansar mkogwaro, kansar ciki, kansar wurin da abinci ke wucewa zuwa hanji, sai kuma kansar mahaifa.

 

Albasa tana tacewa jinin jikin ‘Dan Adam. Duk mutumin da yake fama da matsalar karancin jini, ya yawaita cin
albasa. insha Allahu jininsa zai
yawaita.

Albasa na rage sikarin dake cikin  Jini wanda ya kunshi sikari mai yawa(hyperglycemia) wannan yana kasancewa ne, lokacin da jinin da ke cikin sikari da ake kira (glucose), yayi yawa fiye da yadda jiki ke bukata, domin yin aiki da shi kamar yadda aka saba. Wannan yanayi shi ne ke samar da matsala nan da nan kuma wadda ke daukar dogon lokaci. Amfani da Albasa kusan kullun ya nuna cewar tana sa sikarin da yake cikin jini ya ragu, saboda ta kunshi wani sinadarin allyl prppyl disulfide, wanda yake taimakawa, wajen rage yawan glucose, ya kuma kara yawan sinadaran insulin.

 

Tana Kara Karfin Sinadaran dake taimakawa wajen yakar cutar Kamar yadda Anne Maune anda shi kwararre ne danagne da kayayyakin abincin, mai zama a Washington DC, ya bayyana cewar akwai poly phenolds a cikin albasa wanda yake aiki kamar sojojin da ke yakar cutar cuta da ake kira free radicals.

mata masu zubewar gashi duk matar da
take fama da zubar gashi ko
kwarkwata ko amosani ta samu
man albasa da Man ridi da kuma garin Baqadunas ta kwaba ta rika shafawa a matsirar gashinta kullum kafin ta
kwanta barci da safe sai ta
wanke da ruwan zafi ta ci gaba da yin haka har tsawon kwana bakwai

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *