fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Amfanin Ayaba ga lafiya da yadda ake sarrafata domin maganin kurajan Fata da sauransu

Wani bincike da nazari da masana su ka gudanar kan amfanin ayaba ga lafiyarmu, ya gano cewa, ayaba na kunshe da sandarin ‘Fibre’ mai yawa, wanda haka ya sanya cin ta akai-akai kan inganta lafiyar zuciya. Mafi yawan kayan abinci da ke kunshe da wannan sandari na ‘fiber’ suna da muhimmmanci ga zuciya.

Bisa ga wani bincike da Jami’ar Leeds ta kasar Burtaniya ta gudanar, ya nuna cewa, yawan amfani da abinci mai kunshe da sanadarin fiber-irin su ayaba na iya ragewa mutum haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya.

Kadan daga cikin tasirin Ayaba da Bawonta ga lafiya.

Manazarta, sun tabbatar da cewa, daga cikin amfanin ayaba ga lafiyar dan adam, akwai taimaka wa wajen saurin narkar da abinci. Saboda haka ne, su ka bada shawara ga jama’a su yawaita cin ayaba don su sami lafiyar cikinsu, da ma sauran jikinsu gaba daya, saboda saurin narkar da abinci na sanya wa abinci ya yi tasiri a jikinmu cikin gaggawa.
Ayaba na taimakawa wajen sanya hakoranmu haske; bayan an wanke baki da magogi, sai a samu bawon ayaba a goga a kan hakorin. Idan ana yin haka na tsawon mako biyu za a ga cewa hakoran sun kara haske.

Masu yawan kurajen fuska da na jiki, sai a samu bawon ayaba ana shafawa a fuska da jiki a kullum kafin a kwanta barci. Washegari sai a wanke. Za a ji sauki a cikin kwanaki kadan.

Bawon ayaba na magance kaikayin fata. A shafa bawon a kan kurajen.

Ayaba na magance cizon kudin cizo a jiki. Kudin cizo na yi wa fata lahani sosai don haka, sai a samu ayaba a shafa a wajen da aka yi cizon.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *