fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Amfanin Darbejiya ga lafiyar Dan Adam da yadda ake sarrafata domin magance matsanancin Basir da sauransu

Ana amfani da ganyen darbejiya da sassakenta da hurenta da kuma Diyanta duka a matsayin magani. Sai dai ba a fiye amfani da saiwarta a matsayin maganin da ake sha ba saboda hatsarin dake tattareda shi.

Darbejiya na Dauke da wasu sinadirrai masu matuKar muhimmancin da karfin gaske waDanda samuwarsu ya maida darbejiya magani a gida. Ga kaDan daga cikin su :

Sodium, Potassium, Salts, Chloriphyle, Calcium, Phosphorus, iron, Thiamine, Nicocine, Bitamin C, Carotene, ODatic Acid, Gliserida Acid, Asetilolsifuranil, Dekahidro Tetramatil, Okanone, Fenantone, Acetate Acid da sauransu.

Yadda ake Amfani Da Darbejiya.

Ciwon Suga: A nemi Diyan darbejiya misalin rabin gwangwanin madara sai a saka ganyen manguro fresh, mangoe leaBes kwara uku a tafasa da kyau a misalin cup Daya sai a sha da safe bayan an karya.

Gudawa: Idan an ci wani abinci ko abin sha da ya gurBata ciki to sai a tafasa ganyen darbejiya, a tsayaye ruwan na farko a sake zuba wasu a tafasa sai ga na biyun za a iya tarfa zuma kaDan sai a sha.

Ciwon Hanta: Duk da yake ita hanta ba ta son abu mai Daci kuma yawan amfani da kayan Daci na illatata amma indai za a kiyaye da yanda ake sha to wannan maganine. Anan Diyan darbejiya ne ake amfani da su inda za a tafasa rabin gwangwanin timatir karami a tace da kyau a tarfa gangariyar zuma sai a sha da safe.

Malaria: za a iya shan ruwan ganyen darbejiya dai-dai kada a sha da yawa, a rinKa shan kaDan-kaDan saboda za ka iya amai. Kuma ana son su tsaya a jikinka dan su yima aiki. Daga bisani ana iya tafasa ganyen sai a yi wanka da ruwan ko a yi suraci da su.

Basir Mai Tsiro: A duk sanda basir ya Daura maka aure yana ta wahalda kai inda yake haifar maka da fitar baya ko tsanin zafi da ko tsagewar dubura ko wahala a yayin bayan gari da zubar jini da jin KaiKayi a dubura to ka ne mi sassaken darbejiya dana gasgery ka wanke da kyau ka tafasa ka sha kuma za ka iya zama a cikin ruwan inda za ka tsoma duburarka a ciki tsawon mintuna goma ko fiye a kullum sau biyu safe da yamma har basir Din ya zuKe. Haka kuma za ka dake garinsu ka gauraya da man shafi na Baseline sai ka wanke wajen da kyau ka rinKa shafawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *