fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Amfanin Tufah ga lafiyar jikin Dan Adam

Tufah na dauke da sinadarin ‘Vitamin C’ duk da dai sinadarin na cikinsa kadan ne amma akwai wasu sinadarai wadanda su ma aikinsu dai dai yake da wannan sinadarin a cikinsa, wanda suke haduwa su taimakawa hanji wajen kare shi daga cutar Daji wato ‘Cancer’ a Turance wanda a yau ake fama da ita a duniya. Yana kuma taimaka zuciya daga bugun da ya wuce ka’ida.
Tuffah ko Apple yana taimakon dasashi wajen kare shi daga cinyewa ya karfafa hakori, ya kare harshe daga wata cuta da ake kira ‘Mouth Cancer,’ wato Cutar Dajin Baki. Haka kuma taunashi da hakori ba irin na yangayu sai an datsa da wuka ba yana taimakawa wajen haskaka hakori. Wanda ke fama da ciwon kai musamman na gajiya ko damuwa, yana iya fereye shi ya cinye banda bawon, ciwon kan zai sauka.
Ga masu matsalar kumewar ciki za su iya goga shi a abin goga Kubewa da bawonsa, su murza ganyen na’a na’a, su tace ruwan su zuba akai su zuba Zuma cokali biyu, su rika shansa da safe kan su karya na sati guda in suka yi a jere da yardar Allah za su rabu da matsalar. Kowanne dan ita ce in aka yanka shi aka bar rabi, ya yi duhu amfaninsa ya kare amma Apple ya bambanta domin amfaninsa ba ya karewa indai ba rubewa ya yi ba. Don haka ko kin yanka sai, kika ga yayi ruwan kasa wato ‘Brown’ saboda ajiye shi da aka yi, in dai a waje ne rufaffe mai tsafta, to a yi amfani da shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *