fbpx
Friday, January 21
Shadow

An ɗauke ɗalibin Jami’ar Bayero Da Ke A Jihar Kano

INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

An ɗauke ɗalibin Jami’ar Bayero Da Ke A Jihar Kano

An ɗauke ɗalibin Jami’ar Bayero Kano, BUK, Shafi Auwal Muhammad, ɗan aji 2 da ya ke karantar Ilimin Fasahar Fetur a jami’ar.

Iyayen ɗalibin sun baiyanawa Daily Nigerian Hausa cewa ya bar gida tun a ranar Alhamis, amma kuma an ɗauke shi a tsakanin Tsohuwar BUK zuwa Sabuwar BUK.

Iyayen na sa sun ce har yanzu ba a tuntuɓe su ta waya a kan Muhammad, ko gano inda ya ke ba.

Haka-zalika Ƙungiyar Ɗalibai ta BUK, a wata sanarwa mai ɗauke da Shugaban ta na riƙon ƙwarya, Auwal Lawan Nadabo, ta tabbatar da ɓatan ɗalibin.

A sanarwar, ƙungiyar ta ce bayan samun labarin ɓatan Muhammad, ta tuntuɓi abokan karatun sa, waɗanda su ka tabbatar da cewa bai zo makaranta ba bayan ya bar gida, inda ta ƙara da cewa duk layikan sa na waya ba sa aiki.

Ƙungiyar ta ce duk wanda ya gan shi ko ya samu wani labari a kan sa to ya tuntuɓi 08064178848.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a Bara ma an samu rahoton ɗauke wata ɗalibar jami’ar, wacce a ka ɗauke a kan hanyarta ta zuwa Sabuwar BUK, amma daga bisani a ka tsince ta a wani gida a unguwar Sabongari a cikin birnin Kano.

Haka-zalika yau kwanaki 3 kenan da ƴan bindiga su ka kutsa kai gidan mahaifiyar tsohon ɗan majalisar wakilai ta Kano, mai wakiltar Gezawa, Isyaku Ali Danja, inda su ka yi awon-gaba da ita.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *