fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

An bayyana lokacin da gwamnatin tarayya zata sallami ma’aikatan N-Power Dubu 200 daga aiki

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin sallamar ma’aikatan N-Power na farko da aka dauka su 200,000 daga aiki inda za’a samar musu wata damar samun aikin ko kuma sana’a ta daban.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ta ji daga majiya me karfi daga ma’aikatar kula da walwalar jama’a da Ibtila’i ta kasa cewa ana shirin sallamar Ma’aikatan N-Power dinne tsakanin wasan Janairu zuwa Fabrairu na wannan shekarar da muke ciki.

Majiyar ta kara da cewa tun a shekarar 2018 lokacin ma’aikatan N-Power din ya kare amma saboda ana tsaka da shirin zabe bai kamata a sallami mutane 200,000 daga aiki ba shine dalilin da yasa aka barsu suka ci gaba da aiki inda a yanzu sun kara watanni 16 akan watannin da tun farko ya kamata su yi.

Rahoton ya kara da cewa, sallamar ma’aikatan N-Power din ta zama Dole lura da cewa babu tanadin albashinsu a cikin kasafin kudin shekarar 2020.

Saidai akwai tsarin da ake musu na samar musu da bashin Naira dubu 30 zuwa 100 dan kada su koma zaman banza su dogara da kansu,hakanan gwamnati na tattaunawa da jihohin da suka amfana da aikin N-Power da su dauki ma’aikatan da suka nuna hazaka a aikin. Akwai kuma tsarin samarwa wasu ma’aikatan N-power din ayyukan tsaro na Civil Defence, Da hukumar shige da fice ta kasa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *