fbpx
Thursday, December 2
Shadow

An biya diyya ga rashin wasan Ronaldo a Koriya

Wata kotu a Koriya ta Kudu ta umarci wadan da suka shirya wasan sada zumunta da Juventus da su biya mutum biyu diyya.

An sayar da tikitin kallon wasan sada zumunta tsakanin Juventus da fitattun ‘yan kwallon Koriya da cewar Ronaldo zai buga karawar, amma bai shiga wasan ba.
An umarci wadan da suka shirya wasan, The Fasta da su biya mutum biya fam 240.
Cikin kudin diyyar fam 194 ya shafi damuwa da tashin hankali da dimuwa da mutanen suka shiga wadan da ;yan gani kashe din Ronaldo ne in ji Lauya, Kim Min-ki.
Kim, wanda ya shigar da karar ya ce The Fasta sun yaudari mutane da sunan Cruistiano Ronaldo don amfanar kansu.
Ya kara da cewar ”Ga magoya bayan Ronaldo wannan kamar rashin dan kwallo ne da suke marawa baya tsawon rayuwarsu.”
Kim ya shaidawa Reuters cewar yana wakiltar wasu mutum 87 da za su shigar da kara da ta shafi kin saka Ronaldo a wasan sada zumuntar da aka tashi 3-3.
Cikin minti uku aka sayar da tikiti 65,000 tare da tallar cewar Ronaldo mai shekara 34 zai fafata a wasan.
Magoya baya sun harzuka da suka tabbatar cewar Ronaldo ba zai buga wasan ba, inda suka dunga kiran sunan abokin hamayyarsa Lionel Messi.
Ita ma kungiyar kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa na Koriya ta Kudu sun aike da wasika ga Juventus kan karya yarjejeniyar da suka kulla.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *