fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

An Cafke Wasu Masu Ba da Bayani ga ‘Yan Bindiga 6 A Jihar Neja

Jami’an tsaro sun kama wasu mutane shida da ke kaiwa’ yan bindiga bayanai a jihar Neja.
An ce wadanda ake zargin suna da alhakin ciyar da ‘yan ta’adda da bayanai game da motsin jami’an tsaro.
An kama masu gabatar da bayanan a kananan hukumomin Shiroro da Munya na jihar.
A cewar wata majiyar tsaro, an cafke wadanda ake zargin ne a yayin da suke kan hanyarsu ta ba da bayanai game da motsin sojojin da aka tura zuwa yankunan ga ‘yan fashin.
Wani likita, wasu matasa da manoma an ce suna cikin wadanda aka kama.
Wata majiyar tsaro, wacce ta zanta da Aminiya, ta ce a yanzu haka masu gabatar da bayanan suna hannun ’yan sanda suna gudanar da bincike a kansu don tabbatar da laifinsu ko akasin haka kan abin da ake zargi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ba a same shi ba saboda wayarsa a kashe take har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *