fbpx
Monday, October 25
Shadow

An dakatar da ni ne saboda nina fara maganar tsige Shugaban Majalisa – Dan Majalisar jihar zamfara

Daya daga cikin ‘yan majalisar biyu da majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar, Hon. Yusuf Mohammed Anka, mai wakiltar mazabar Anka ya koka da cewa dakatar da shi bai rasa nasaba da rawar da ya taka a kokarin tsige kakakin majalisar, Hon. Nasiru Mu’azu Magarya.

A cewarsa, ya fara wannan yunkuri ne watanni biyu da suka gabata cewa tilas ne a dakatar da kakakin majalisar saboda gazawar sa na jagorantar majalisar kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

Dan majalisan ya shaidawa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar cewa tun daga lokacin kakakin majalisar bai ji dadinsa ba saboda fara tsige shi, wanda ya bayyana a matsayin makirci.

Dan majalisar ya kara da bayyana cewa Gwamnan da kansa ya kira tare da yi masa barazana kan matakin tsige shi, inda ya nuna cewa duk kokarin da aka yi na barin Gwamnan ya fahimci gazawar Kakakin Majalisar abin ya tura.

Ya bayyana cewa bayan wasu kwanaki, Gwamnan ya umarci tsohon ministan kudi, Bashir Yuguda da ya sasanta tsakanin kungiyar, domin su dakatar da niyyarsu kuma saboda tsoma bakin tsohon ministan, Yuguda, an dakatar da matakin.

Dan majalisar ya ce yana da kwarin gwiwa cewa kwamitin da’a da alfarma zai yi masa adalci da abokin aikinsa.

Ya kara da cewa ya kuduri aniyar gurfanar da majalisar dokokin jihar a gaban kotu saboda bata masa suna da kuma lalata sunansa da mutuncinsa.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *