fbpx
Saturday, October 16
Shadow

An dakatar da shugaban Islamiyyar da aka lakada wa ɗaliba duka a Kwara

Gwamnatin jihar Kwara a Najeriya ta dakatar da shugaban wata makarantar arabiyya da wani bidiyo ya nuna an kewaye ɗaliba ana lakada mata duka saboda saɓa dokar makarantar.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce an dakatar da shugaban makarantar ne bayan wata tawagar gwamnati da ta kunshi kwamishinan ilimi da mai ba gwamna shawara kan harakokin addinin Islama sun ziyarci Islamiyyar.

Bidiyon da gwamnatin ta wallafa a Facebook ya nuna yadda wasu maza suka sa ɗaliba tsakiya suna lakada mata duka.

Gwamnatin jihar Kwata ta ce ta naɗa kwamitin binciken al’amarin da ya ƙunshi malaman addini da jami’an gwamnati.

Sanarwar dai ba ta bayyana dalilin da ya haddasa yi wa ɗalibar duka ba da kuma lokacin da al’amarin ya faru.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *