fbpx
Thursday, July 29
Shadow

An gano cewa, Mutuminnan farar fata da aka kama me baiwa ‘yan Bindiga horo, Tsohon Sojan kasar Faransa ne

Mutuminnan da kwanaki labarinsa ya karade kafafe da yawa wanda aka kama a kasar Africa ta tsakiya, CAR, tsohon Sojan Faransa ne.

 

An kuma Gabo cewa, Tun a shekarar 2013 ya ke baiwa ‘yan Bindigar kasar,CAR horon yaki, a yanzu dai a karin farko an Gurfanar dashi gaban Kotu.

 

Wasu na tunanin kasar Faransa ba zatavrasa Masaniya da wannan mutumin ba, dalili kuwa shine, kasar CAR ta kawar da akalarta daga kasar faransa zuwa Rasha wajan neman taimako kan harkar tsaro.

 

Wannan dalili yasa wasu ke tunanin Faransar ta aiko irin wancan mutumin dan ya gurgunta alakar kasar CAR da Rasha.

 

Faransa na kara samun tawaya a dangantakarta da kasashen Nahiyar Africa.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *