fbpx
Saturday, December 4
Shadow

An gano dalilin da mata ke kashe mazajan su

Wani masanin zamantakewar halayyar dan Adam a jami’ar Bayero ta Kano, Dr. Sani Lawan Malumfashi, ya bayyana yawaitar kashe-kashen da ake samu tsakanin ma’aurata cewa na da alaka da rashin daidaiton koyi da kyawawan hallaiyar manzon Allah S.A.W.

Malumfashi, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da gidan rediyon Dala a yau Litinin.
Ya kuma kara da cewa” Akwai yawan karatu tsakanin al’umma, amma kuma babu ilimi duk da yawaitar makarantun da a ke da su wanda hakan na kara taka rawa wajen samun kisa a tsakanin ma’aurata”.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A nasa bangaren Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu, cewa ya yi” al’amuran kisan kai tsakanin ma’aurata ya na da alaka da hassada a tsakanin juna”.

Haka zalika, sun kuma bukaci iyaye su maida hankali wajen tabbatar da cewar ‘ya’yan su sun samu karatu da kuma ilimin zamantakewar aure kafin aurar da su.
DalaFM


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *