fbpx
Sunday, September 26
Shadow

An gano dan ta’addar da ya harbo jirgin yakin Sojojin Najeriya a jihar Zamfara

Rahotanni sun bayyana wani me suna Ali Kachalla a matsayin Wanda ya harbo jirgin saman yakin sojojin Najeriya a jihar Zamfara.

 

Rabar 18 ga watan Yuni ne dai aka harbo Jirgin ta hanyar amfani da muggan makamai. Sanarwar da hukumar sojojin Najeriya ta fitar, bata bayar da cikakken jawabin yanda lamarin ya faruba.

 

Saidai Daily Trust ta ruwaito cewa, ta samu bayanai daga mutanen yankin da kuma wasu jami’an tsaro dake da masaniyar yanda dazukan jihar Zamfara suke.

 

An bayyana Kachalla a matsayin matashi dake tsakanin shekaru 30 zuwa sama sannan kuma an ce yana da yara masu aiki a karkashinsa da suka kai 200.

 

Yana boyene a kauyen Goron Dutse dake da nisan Kilometres 25 daga garin Dansadau na jihar Zamfara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *