fbpx
Thursday, July 29
Shadow

An gano Gwamna Wike ya baiwa jami’an INEC cin hancin Miliyan Dari uku da sittin a zaben 2016

Jami’in dansanda da ya bayyana a gaban majalisar wakilai, Joseph Egbonike ya bayyana cewa a zaben 2016 da aka yi a jihar Rivers, Gwamna Nyesome Wike ya bayar da cin hancin Naira Miliyan 360 ga jami’an INEC.

 

Kudin dai a cewa dansandan me mukamin DIG, an raba su ne ga jami’an INEC 23. Saidai yace sun samu nasarar kwato Miliyan 114,290,000 daga cikinsu.

 

Ya bayyana cewa Wike ya bayar da kudin ne dan a yi murdiyar zabe.

 

Yace an yankewa jami’an INEC din hukunci amma saidai sun daukaka kara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *