fbpx
Monday, November 29
Shadow

An Gano Motocin Alfarma Guda Dari Na Bilyoyin Naira Da Tsohon Gwamnan Zamfara, Yari Ya Karkatar

Kwamitin bin diddigi domin tabbatar da aiyukan gwamnati a jihar Zamfara ya gano wasu motocin alfarma fiye da 100 da tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari, ya saya a kan biliyoyin kudi, inda ya rabawa ‘yan uwa da abokansa.

A cikin wata sanarwa da ta fito ranar Talata daga ofishin Zailani Bappa, mai taimaka wa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a kan harkokin sadarwa da yada labarai, ya bayyana cewa shugaban kwamitin, Ahmed Gusau, ne ya sanar da hakan a cikin rahoton ‘somin tabi’ da kwamitin ya mika wa gwamnan.
A cewar rahoton, tsohuwar gwamnati a karkashin Yari ta gaza nuna inda fiye da motoci 100, kwatankwacin kaso 66% na motocin da gwamnatin jihar ta mallaka, suke bayan karewar wa’adinta.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *