fbpx
Monday, November 29
Shadow

An gano wani babban sirrin Boko Haram

Wasu shugabanni na Amurka sun gano yadda mayaƙan Boko Haram da ke ayyukansu a Arewa maso gabashin Najeriya ke haɗa kai da ƴan fashin dajin da ke kai hare-hare a arewa maso yammacin ƙasar wajen satar mutane don kuɗin fansa daga hannun gwamnati da fararen hula, kamar yadda jaridar Wall Street Journal ta ruwaito.

Jaridar ta ƙasar Amurka ta ruwaito cewa Amurka ba ta ganin fashin daji a matsayin barazana a gareta, amma jami’ai sun jima suna sa ido kan kwamandojin ƴan bindiga da yiwuwar alaƙarsu da mayaƙan Boko haram.

Wani rahoto da jaridar ta wallafa ranar Asabar ya ce “Amurka ba ta wani damu ƙwarai ba da ƴan fashin daji, duk da cewa jami’an gwamnatin Amurka sun ce sun yi kutse kan wani kiran waya daga wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne da ke arewa maso gabashi kuma an ji suna bai wa ƴan bindiga a arewa maso yammacin ƙasar shawara kan garkuwa da mutane da tattaunawa don karbar kuɗin fansa.”

Rahoton ya kuma jaddada kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana ƴan fashin dajin a matsayin ƴan ta’adda, duk da cewa ba su da wani buri na siyasa ko addini.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *