fbpx
Monday, September 27
Shadow

An gano wata makarkashiya ta sanya Man fetur yayi tsada a Arewa fiye da kudu:An roki Shugaba Buhari ya dauki mataki

Gamayyar kungiyoyin farar hula na Arewacin Najeriya ta yi zargin cewa kudurin dokar da `yan majalisar dokokin kasar suka zartar a kan inganta harkar man fetur na cike da wasu kura-kurai, wadanda za su iya cutar da al`ummar da ke yankin arewacin kasar.

Kungiyar ta ce ta hada kai da wasu kwararru wajen nazarin kudurin dokar, kuma ta fahinci cewa mai zai yi tsada a arewa fiye da kudancin kasar sakamakon dawainiyar da ke cikin dakonsa.

Ta ƙara da cewa tanadin da aka yi a cikin kudurin na amfani da kashi talatin cikin dari na ribar da kamfanoni za su samu wajen hakar mai a tudu ba zai biya muradin hakar mai a arewacin kasar ba, saboda haka bai kamata Shugaba Buhari ya sa hannu a kan kudurin dokar ba.

Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar, Nastura Ashir Shariff, ya shaida wa BBC Hausa cewa sun lura akwai zunzurutun rashin gaskiya da ban tsoro a cikinsa, don haka ba za su amince da shi ba.

”A zo a ce za a dauke wannan kasuwar man fetur a cire dukkan ma’aikatu uku da suke kula da farashin man nan a tattara a danka a hannun wani kamfani na wani dan kasa mutum daya, wannan akwai rashin adalci a ciki” in ji shi.

Ya ƙara da cewa babu abun da hakan zai haifar illa tsadar man fetur ga al’ummar arewa saboda sai an yi dakon man daga kudu za a kai yankin, abin da zai haifar da wahalarsa a arewacin Najeriya.

Ya ce: ”A cikin farashin man fetur din nan da ake siyarwa Naira 165 ko 167 ana biyan kusan fiye da Naira 8 a matsayin kudin da ake cirewa na dakon man fetur, ka ga babu gaskiya a ciki, kuma an tabbatar da cewa talaka za a cuta a ciki.”

”Mu kiranmu ga Shugaba Muhammadu Buhari shi ne kada ya yadda ya sa hannu a wannan doka, domin idan aka yi haka ba abun mamaki ba ne, misali, a rika sayar da lita Naira 10 a kudu, a arewa kuma Naira 25 ba”

Kungiyar ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar wa majalisar dokokin Najeriya wannan doka kamar yadda ya sha yi a baya, domin ta sake duba ta, ta yi abin da ya dace ga kowa da kowa.

”Shugaban kasa yana da ikon da zai yi haka, domin tabbatar da cewa ba a sayar da Najeriya ga ‘yan kasuwa da ‘yan jari hujja ba” a cewarsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *