fbpx
Friday, May 14
Shadow

An guntule mazakuta da Marainan wani aka baiwa Alade ya cinye bayan da yayi yunkurin yima wata ‘yar uwarsa Fyade

Wani mutum dan Shekaru 36 ya gamu da jafa’i bayan da aka guntule mazakutarsa hadda marainan aka baiwa alade ya cinye.

 

An masa hakane bayan zargin yunkurin yiwa wata ‘yar uwarsa Fyade. Aikuwa Saurayin waccan ‘yar uwar tasa bai yi wata-wata ba ya saka wuka ya yanke masa al’aura ya baiwa Alade.

Mutumin yayi mankas da Giyane inda ya dawo gida ya afkawa ‘yar uwar tasa, saida ta samu ta kubuta inda ta tsere, daga nan kuma kuma shi sai bacci ya daukeshi.

 

Ko da saurayinta ya samu Labari, sai ya kira wani dan uwansa, suka gayyaci yayan budurwar tasa zuwa wata gonar rake inda a nan ne suka masa aika-aika, maimakon zuwa wajan ‘yansanda.

 

Lamarin ya farune a yankin Olhos D’Agua na kasar Brazil. An garzaya da mutumin Zuwa Asibiti inda daga baya aka samu aka hada masa yanza zai yi fitsari, amma dai Likitocin sun ce da wuya a mayar masa da mazakutarsa.

 

Jami’in Dansanda, Michael Stephen Da Silva ya bayyana cewa, sun nemi mazakutar mutumin amma ammu ganta ba inda aka yi ifakin, Aladun aun cinyeta.

 

Saidai an kama wadanda ake zargi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *