fbpx
Sunday, September 19
Shadow

An gwabza fada tsakanin Taliban da mayakan da basa goyon bayansu an kashe daruruwan ‘yan Taliban din

Rikici ya ƙara kazancewa a Afghanistan tsakanin Taliban da mayaƙan da ke riƙe da lardin ƙarshe na ƙasar da Taliban ɗin ba su ƙwace ba.

Dubban dakarun Taliban ne suka ƙaddamar da hari kan mayaƙan a lardin Panjshir, lardin da tsohon mataimakin Afghanistan da tohon ministan tsaron ƙasar suka koma bayan birnin Ka’bul ya faɗa hannun ƴan Taliban ɗin.

Mayaƙan sun ce sun fatattaki dakarun Taliban ɗin tare da kashe ɗaruruwansu.

Ko a jiya Alhamis, sai da kakakin Taliban ɗin ya ce dakarunsu sun shiga lardin tare yi wa mayaƙan mummunar illa.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *