fbpx
Monday, November 29
Shadow

An hana ɗan tsohon shugaban Libya tsayawa takarar shugabancin Libya

Hukumar zabe a Libya ta cire sunayen ‘yan takara 25 daga cikin wadanda ke neman kujerar shugaban kasa a zaben da za a yi a watan gobe, ciki kuwa har dan tsohon shugaban kasar marigayi Mu’ammar Gaddafi Saif al-Islam.

Yan takara 73 ne suka cika ka’idojin da ake bukata domin shiga zaben, an kuma ba da damar daukaka kara ga wadanda aka cire sunayensu idan matakin bai gamsar da su ba.

An cire sunan Saif al-Islam ne sakamakon nemansa ruwa a jallo da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke yi, kan zargin aikata laifukan yaki.

Dokokin zaben Libya sun haramtawa duk wanda ake tuhuma da aikata laifi tsayawa takara har sai idan kotu ta wanke shi ga wannan laifin.

Wata kotu a birnin Tripoli ta yankewa Saif al-Islam hukuncin kisa, kan laifukan da ya aikata a lokacin juyin juya halin da ya hambarar da mulkin mahaifinsa Mu’ammar Gaddafi a shekarar 2011. Amma daga bisani sabuwar gwamnatin ‘yan adawa da ke gabashin Libya ta yi ma sa afuwa.

Hukumar zaben ta ce dalilin da ya sa aka cire ‘yan takara 25, shi ne samun bayanai daga masu shigar da kara na gwamnati da kotuna, da sufeton ‘yan sandan Libya da na hukumar shige da fice kan mutanen da har yanzu ba a kammala yi musu shari’a ba.

Haka kuma cikin wadanda ake ta cece-kuce tun bayan sanar da aniyarsa ta tsayawa takara har da Janaral Khalifa Heftar, wanda masu sharhi ke ganin shairdarsa ta zama dan Amurka ka iya taka rawa wajen hana shi takarar.

A makon da ya gabata dubban ƴan kasar ne suka yi zanga-zanga a birnin Tripoli, domin nuna adawa da tsayawar ‘yan takarar da ake yi wa shari’a.

Har wa yau, cikin ‘yan takarar da za su fafata akwai tsohon Firaminista Abdel Hamid Dabaib da tsohon ministan cikin gida Fathi Bashagha, dukkansu hukumar zabe ta ce sun cika sharuddan tsayawa takara.

Tun da fari, jakadun kasashen Amirka da Birtaniya da Faransa da Jamus da Italiya a kasar Libya sun yi kira da dukkan ƴan siyasar su mutunta matakin da hukumomi suka dauka.

A bangare guda kuma kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da goyon baya ga matakin da hukumar zabe ta dauka kan yadda za a gudanar da zaben shugaban kasar akan lokaci.

Kawamitin ya kara kira ga ‘yan takara su amince da sakamakon zaben a duk yadda ya zo, idan su na da ja su bi hanyar shari’a wajen neman hakkinsu, da mutunta ‘yan adawa a lokacin zabe.

A farkon watan Disamba ake sa ran wallafa sunayen ‘yan takara da zarar an kammala tantance su, sannan wadanda suka daukaka kara sun kammala da kotuna.

A baya an ware ranar 24 ga watan Disambar 2021 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a Libya, wanda shi ne na farko cikin shekaru 10 tun byan hambarar da mulkin marigayi Mu’ammar Gaddafi.

Sai dai a farkon watan Oktoba ‘yan majalisar suka raba zabukan, inda za a yi na su a watan Junairun 2022.

Daga BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *