fbpx
Monday, November 29
Shadow

An kafa kwamitin yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shugaban majalisar dattawa a Najeriya Ahmad Lawan a ranar Alhamis ya kafa kwamitin mutum 56 domin yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar Ovie Omo Agege.

Sannan kuma ya kunshi wasu manyan jami’an majalisar guda takwas – sanata daya daga jihohi 36 sannan da mambobi biyu da ga yankuna shida da ake da su a kasar.

Wasu daga cikin mambobin kwamitin sun hada da shugaban masu rinjaye na majalisar Yahaya Abdullahi, da mataimakinsa Farfesa Robert Ajayi Boroffice.

Akwai kuma shugaban marasa rinjaye Eyinnaya Abaribe da mataimakinsa Sanata Emmanuel Bwacha


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *