fbpx
Sunday, September 19
Shadow

An kama ɗalibai 6 kan yi wa wani mutum ‘askin dole’ a Jigawa

‘Yan sanda a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya sun kama wasu ɗalibai shida kan zargin kutsa kai gidan wani mutum da yi masa askin dole.

Kakakin ƴan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Dutse.

Ɗan sanda ya shaida cewa an kama ɗaliban da ake zargi a ranar 27 ga watan Agusta, bayan Ibrahim Sambo, mazaunin unguwar Yalwawa a Dutse ya shigar da kara.

Mutumim ya ce sai da ya yi zazabin kwana biyu bayan faruwar al’amarin.

ASP Lawan ya ce yanzu haka suna rike da ɗaliban da shekarunsu ke tsakanin 18 zuwa 19.

Wadanda ake zargi sun amsa laifinsu, don haka a cewar kakakin za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *