fbpx
Friday, May 14
Shadow

An kama basarake a jihar Benue da muggan makamai, Dayan Basaraken ya tsere ta kofar baya

Sojojin rundunar Operation Whirl Stroke sun kai samame kan Fadar wasu sarakunan gargajiya 2 a jihar Benue.

 

Lamarin ya farune a karamar Hukumar Ukum ranar Asabar, kamar yanda Tribune ta ruwaito.

 

Wanda aka kama din shine Utambe Adzer wanda kuma Shine hakimin garin Cha. Saidai dayan basaraken, Cheif Teran Kwanghbo ya tsere ta kofar baya, bayan samun bayanan sirri cewa an kama dan Dayan sarkin.

 

Sojojin sun kai samamenne bayan samun bayanan sirri akan sarakunan. Cikin makaman da aka gano a hanun Basaraken Kawai Bindigar AK47 da wata hafin gida da kuma Albarusai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *