fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

An kama budurwa da saurayinta bisa laifin sata da siyar yara kanana a Jihar Ondo

An kama wata mata mai suna Titilayo Kudaisi da saurayinta, Oluseyi Akinsete mai shekaru 31 da laifin sata da sayar da yara.

An damke su ne a Ondo bayan sun saci jariri dan watanni shida a yankin Odo-Ota Sawmill da ke Ilorin, jihar Kwara.

Bayan an yi mata tambayoyi, ta amsa cewa ta sayar da jarirai biyu a jihar Imo kan N500, 000 da N300, 000.

Ta kuma yi ikirarin cewa saurayin nata ne ya gabatar da ita ga sana’ar.

Kwamishinan ‘yan sanda na Ondo, Bolaji Salami wanda ya gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai ya ce nan ba da dadewa ba za a gurfanar da su a kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *