fbpx
Thursday, September 23
Shadow

An kama iyayen da suka yi karyar cewa an sace diyarsu dan su samu kudin biyan bashi

Jami’an tsaro a jihar Delta sun kama wasu ma’aurata da suka yi karyar cewa an sace diyarsu dan su samu kudin biyan bashin banki da suka karba.

 

Diyar tasu, Stephine Oghenevoke me shekaru 21 na aiki ne da bankin Heritage inda ta taimaka musu suka samu bashin Miliyan 17 dan yin kasuwanci.

 

Saidai kudin sun lalace ba tare da samun damar biyan bashin ba, an zargesu da shirya cewa an sace diyarsu dan su samun kudin biyan bashin. Tuni dai ‘yansanda suka kama iyayen da diyar dan bincike.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *