fbpx
Friday, April 23
Shadow

An kama Magidanci da ya kashe kwarton da ya kama da matarsa

Wani magidanci dan kimanin Shekaru 30 ya kashe kwarton da ya kama tare da matarsa.

 

John Samuel ya kashe Yaji Lawal me kimanin Shekaru 57 saboda zargin yayi lalata da matarsa.

 

Lamarin ya farune a kauye Bandasarga dake karamar hukumar Ganye ta Jihar Adamawa.

 

‘Yansanda sun bayyana cewa john ya koma gidansa da misalin karfe 11:30 na ranar Lahadi inda ya tarar da Lawal ya kuma yi zargin cewa ya jene yayi lalata da matarsa. Nan take kuwa ya daba masa wuka, an garzaya dashi Asibiti inda ya mutu acan.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Sulaiman Yahaya ya tabbatar da faruwar Lamarin, inda yace ana kan bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *