fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

An kama mahaifin da ya kashe ‘ya’yansa 4 bisa zargin cewa bashi ne ubansu ba, Cin Amanarsa matarsa ta yi

Kotu ta yankewa wani Lauya hukuncin daurin rai da rai har nunki 4 saboda kashe ‘ya’yansa 4 bisa zargin cewa ba shine ubansu ba, matarsa cin amanatsa ta yi ta haifesu.

 

Lamarin ya farune a kasar Africa ta Kudu. Kuma kotun dake Limpopo ta yanke masa hukuncinne ranar Juma’a, 4 ga watan Yuni.

 

Shekarun ‘ya’yan nasa da ya kashe 9, 7, 5 da 3. Kamin ya kashe su ya saka sako a facebook inda yace matarsa ta ci amanarsa ta goga masa cutar Kanjamau.

 

Mutumin, Senyatsi Lucas dan shekaru 52 yagi kisanne a watan Fabrairu na shekarar 2020 kuma ya amsa laifinsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *