fbpx
Monday, May 10
Shadow

An kama mai fentin da laifin yin karya da sunan wani basaraken Legas (Oba Elegushi) tare da damfarar wata mata kudi N51m a Facebook

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta cafke wani mai sana’ar fenti, Moses Olaitan, da abokin aikin nasa, Segun Omoshola, bisa zargin bude asusun Facebook na bogi da sunan sarkin Legas na yankin Ikate, (Oba Saheed Elegushi), tare da amfani da hotonsa wajen damfarar wata mata da suka hadu da ita a Facebook kan kudi N51m.

Da yake gabatar da wanda ake zargin gaban manema labarai a ranar Alhamis, 29 ga Afrilu, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Hakeem Odumosu, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan korafin da aka shigar a ofishin.

Ya ce bayan cikakken bincike, ‘yan sanda sun gano tare da cafke Olaitan da Segun watanni uku bayan aikata laifin.

Da yake zantawa da manema labarai, Olaitan yace, bayan ya bude wani shafin Facebook da sunan masarauta kuma ya fara sanya hotuna daban-daban na basaraken don jan hankalin masu neman auren sarki.

Yace; komai ya faru ne a Facebook, yayi kwaikwayon Oba Saheed Elegushi a Facebook kuma yayi amfani da hotunan sa. Ita (wadda abun ya shafa) ta haɗu da shi a kan layi kuma ta ce tana son ta auri sarki kuma sun fara daga can.

Ya gaya mata cewa idan tana son auren sarki, tana buƙatar yin wasu ayyukan al’adu kuma ta yarda.

Nan take ta ce ya tura lambar akawun dinsa, amma saboda ba shi da lambar akawun din, sai ya tuntubi Segun, wanda ya samar da asusun da aka yi amfani da shi wajen karbar kudin.

An turo masa N2.5m kuma a lokacin da aka kawo shii wurin kwamandan ne ya san cewa abinda ta biya shi su ne N51m.

Ya kara da cewa yan sanda kama shi ne ta hanyar bibiyar lambar dan uwansa.

A lokacin da aka kama shi yana shirye-shiryen bikin ranar haihuwarsa, a lokacin jami’an suka damke shi.

Abokin aikin nasa, Segun mai shekaru 48, ya ce ya samu Naira miliyan 3.5 ne kawai daga aikata laifin kuma ya yi mamakin yadda wanda aka abun ya sha tayi ikirarin biyan Naira miliyan 51.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *