fbpx
Friday, May 14
Shadow

An kama manyan barayin awaki 2 a Jihar Adamawa

Yan sanda sun ceto wasu yara biyu da ake zargin’ yan Shila ne daga wasu fusatattun mutane dake kokarin kona su da ransu a jihar Adamawa.

An bayyana cewa wadanda ake zargin biyu, Abdulrahaman Musa mai shekaru 26 da Saidu Ibrahim, 27, sun fito ne daga anguwar Nassarawo a Jimeta / Yola, an kama su ne bayan sun saci awaki biyu a karamar hukumar Girei da ke jihar a ranar Alhamis, 22 ga Afrilu.

A cewar wani wanda abin ya faru a gaban idanunsa, ‘yan Shila sun afka wa garin Girei a kan babur mai kafa 3 inda suka sace dabbobin.

Mazauna garin sun gan su kuma nan take sukai shela jama’a suka fito suka bi bayansu tare da kama su.

Fusatattun mutanen sun yi wa barayin tsinannen duka sosai, da kuma yunkurin cinna musu wuta da ransu kafin yan sanda su kawo masu dauki, amma duk da haka, sai da suka cinnawa babur dinsu mai kafa 3 wuta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce wadanda ake zargin suna tsare kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *