fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

An kama masu dakar nauyin ta’addanci a Najeriya

An kama gwamman mutane da ake zargin na daukar nauyin ta’addanci a Najeriya.

 

Manyan hukumomin tsaron Najeriya ne suka kaddamar da bincike ka kamen mutane 957 da ake zargi da ta’addanci a kasar.

 

Binciken ya kai ga gano wasu asusun bankin mutanen masu daukar nauyin ta’addancin wanda tuni aka dakatar da amfani da asusun bankunan.

 

Daily Trust ta ruwaito cewa, cikin wanda aka kama akwai masu canjin kudi da sauransu daga jihohin Kano, Borno, Abuja, Sokoto, Legas, Adamawa, Kaduna da Zamfara. Zuwa yanzu dai an kama mutane 400.

 

Kuma akwai ‘yan uwan mutanen nan maau canji ‘yan Najeriya dake Dubai da aka ka da zargin daukar Nauyin Boko Haram.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

2 Comments

  • Bashir

    To yanzu wane mataki gwamnati zata dauka akansu bayan sun barnatar da rayukan jama,a yan nijeriya sama da mutane dubu hamin menene amfanin kaisu kotu duk bata lokaci ne amma shawara ta rage wa gwamnatin Buhari’s muna gefe muna kallo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *