fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

An kama masu satar Karfen Titin Jirgin kasa:Gwamnati na shirin saka Hukuncin kisa kan lamarin

Jami’an tsaro a jihar Nasarawa, sun kama masu satar karfen titin jirgin kasa inda kuma suka yi yunkurin bayar da cin hancin Najira 160,000.

 

Barayin sun kammala kwashw karfen titin jirgin kasar inda a daidai wannan lokacine jami’an ‘yansanda suka isa wajan, suna ganinsu sai suka tsere.

 

Amma an kama 2 daga ciki, Mohammed Abdullahi da Abubakar Nuhu, sun yi yunkurin baiwa ‘yansanda  cin hancin 160,000 amma suka ki karba. Kakakin ‘yansandan jihar,  Bola Longe ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

A wani Rahoton me kama da wannan kuma, Ministan sufurin,  Rotimi Amaechi ya bayyana cewa suna duba yiyuwar saka hukuncin kisa kan masu satar karafen titunan jirgin kasa.

 

Ya bayyana hakane a wajan wani taro a Abuja.

 

Yace ba wai ana kallon kudin karafan bane, ana kallon rayukan da za’a rasa idan dalilin satar karafen aka samu hadari, yace tunda suma suna sanadin a mutu, shiyasa suke tunanin kai lamarin gaban majalisa a saka dokar hukuncin kisa akai.

”So imagine you are carrying a train of 14 or 20 coaches with 85 passengers in each coach, if it derails, can you quantify how many passengers that would have died in the course of one man thinking he is making money.

”So, it is not about the cost but the lives that would have been lost because of few interest.

”Some people have recommended that since this people are killing people, if accident happens people will die, so we should go back to the National Assembly and pass a law that does not only criminalise the action but consequences should be death,” he said.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *