fbpx
Saturday, April 17
Shadow

An kama matashi a jihar Adamawa da ya kashe wani ta hanyar caka masa Wuka

‘Yansanda a jihar Adamawa sun kama Yusuf Jibrilla dan shekaru 25 da ya cakawa wasu matasa wuka har daya ya mutu.

 

Lamarin ya faru ranar Litinin 29 ga watan Maris a Mayo-Nguli dake karamar Hukumar Maiha ta jihar.

 

Wanda ya cakawa wukar sune Sadik Hammadandi da Adamu Sulaiman. Ya samesu ne a wajan wani Biki inda ya tsaya kusa dasu ya sha wiwi. Sun gaya masa ya tashi daga wajan saboda basu son warinta, nan ne ya fiddo wuka ya caccaka musu.

An Garzaya dasu Asibiti inda aka tabbatar da Hammadandi ya mutu, Amma Adamu za’a masa aiki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *