fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

An kama Matashiya me shekaru 19 data kashe wani da ya so mata fyade

An kama wata matashiya me shekaru 19 bisa zargin kashe wani mutum me shekaru 40 da yayi yunkurin mata fyade.

 

Lamarin ya faru a kauyen Nyenda na kasar Zimbabwe. Mutumin me suna Sure Tsuro, ya dade yana neman yin lalata da matar, saidai ta ki amince masa.

 

Wata rana ya same ta tana girki inda ya nemi ya afka mata, amma ta ciro icce daga wuta ta kwakkwada masa. Shima ya kwace iccen ya bugeta dashi, daga baya ya fita daga gidan yana dangyasawa, amma a karshe ya fadi, wanda daga nan ya mutu.

 

An kama matashiyar bisa laifin kisa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *