fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

An kama mutane 27 da ake zargi da damfara ta intanet a Jihar Legas

Jami’an Ofishin shiyyar Legas na Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’anci, EFCC sun kama wasu mutane 27 da ake zargi ‘yan damfara ta yanar gizo.

Wadanda ake zargin sune: David Promise, Cyril Okodogbe, Taiwo Femi, Jasa Oghenerwede Frank, Adesokan Ibrahim, Femi Emmanuel Phillip, Jimoh Olayinka Alimi, Anene Dominic, Victor Damola, Israel Attah, Alonge Oluwadamilare, Muhammadu Sani Garba, Luis Fred, da Adu Olaoluwa .

Sauran sune: Precious Utomi, Oladosu Samuel, Andrew John, Olayiwola Ojo, Ekong Samuel Enobong, Oluwakemi Ezekiel, Okewole Segun, Olawale Adekunle, Ajibade Idris Adeniyi, Imeobong-Odion Promise, Karaole Lateef, Rowland Emmanuel, da Nelson Lucky.

An cafke su ne a ranar 9 ga Afrilu, 2021, a yankin Ayobo-Ipaja na jihar Legas, biyo bayan bayanan sirri da Hukumar ta samu game da zargin su da hannu a zamba da ke da alaka da kwamfuta

Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin yayin kamun sun hada da wayoyin hannu, kwamfutocin tafi-da-gidanka, da motocin alfarma.

A cewar EFCC, ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *