fbpx
Friday, April 23
Shadow

An kama mutane 4 bisa laifin satar wayoyi a wajen bikin rantsar da Gwamna Akeredolu

An kama wasu maza hudu da suka kware a harkar sata a shagulgulan bikin, da laifin satar wayoyi a lokacin bikin rantsar da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu karo na biyu a makon da ya gabata.

Taron wanda aka gudanar a International Event and Cultural Center wanda aka fi sani da Dome.

An bayar da sunayen wadanda ake zargin a matsayin Ojo Femi mai shekaru 30, Abiodun Adewale mai shekaru 45, Kayode Olarewaju mai shekaru 45 da Aiwole mai shekaru 25.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an rundunar Operation Scorpion Squad da ke hade da gwamnatin jihar Ondo a kan hanyar Ilesha zuwa Akure ne suka cafke su yayin da suke komawa sansanin su na jihohin Oyo, Osun da Kwara.

An kwato wayoyi bakwai da suka sace a wurin shagalin bikin ƙaddamarwar.

Ojo wanda ya amsa laifin satar wayoyi shida a Dome ya ce abokinsa ne ya ba shi wayar.

Ya kuma ce, ya kan je biki don satar wayoyi kuma yawanci yakan sayar da su kan N8000 zuwa sama.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro, ya ce nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *