fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

An kama mutane 50 da keda hannu akan hare-haren Jihar Imo – Gwamna Hope Uzodinma

An kama mutane hamsin dangane da harin da aka kai kwanan nan a gidan yari na Owerri da kuma rundunar ‘yan sanda a jihar Imo.

Gwamnan jihar, Hope Uzodinma, ne ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa a ranar Juma’a bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamnan ya roki shugaban kasa kan inganta harkokin ma’aikata da kayan aiki ga hukumomin tsaro a jihar.

Uzodimma ya ce, “Kamar yadda muka yi a ƙidayar, mun kame kusan mutane 40 zuwa 50, waɗanda suka amsa laifukansu kuma aka samu bayanai masu amfani a wajen su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *