fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

An kama mutane 7 bisa zargin satar mutane a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta cafke wasu mutane bakwai da ake zargin masu satar mutane ne a garuruwan Zariya da Kaduna.

Kakakin rundunar, Mohammad Jalige, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Laraba a hedkwatar rundunar da ke Kaduna.

Ya ce wadanda aka kama sun hada da wani mai suna Mannir Salihu, wanda aka damke kan kisan wani Idris Bashir, wanda ya bar gidansa na Zariya, a ranar 4 ga Yuni, 2021 kuma bai dawo ba.

Salihu, wanda aka ce aboki ne ga mamacin, ana zargin ya kashe shi ne don gudun kar ya dawo da Naira 385,000.00, wanda ake bin mamacin.

A cewar Jalige, “A ranar 5 ga Yuni, 2021 da misalin karfe 9 ne rundunar ta samu korafi daga wani basarake na garin Zariya cewa a ranar 4 ga Yuni, 2021 da misalin karfe 10 na dare dansa mai suna Idris Bashir ya bar gida bai dawo ba.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *