fbpx
Thursday, September 23
Shadow

An kama mutane biyar da ake zargi da fille kan wata karuwa a Jihar Kwara

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kwara sun cafke wasu mutane biyar da ake zargin matsafa ne bisa laifin kisan wata karuwa a karamar hukumar Patigi ta jihar.

Kakakin rundunar, Okasanmi Ajayi, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Ilorin a ranar Juma’a, 10 ga watan Satumba, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin a matsayin Samuel Peter Tsado, Mohammed Gbara aka Madi, Abubakar Mohammed wanda aka fi sani da Baba Pati, Mohammed Ahmadu Nma da Bala da kuma karin da wasu uku gaba daya.

A cewar PPRO, wanda aka kashe mai suna Abigail an jawo ta ne daga otal din da take aiki, an kai ta gidan daya daga cikin wanda ake zargi sannan aka fille kan ta don dalilai ayi tsafi.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Talatu Assayomo ya tabbatar wa da jama’a tsaron rayukansu da dukiyoyinsu.

Kwamishinan ya bayyana cewa ana iya samun hakan ne kawai tare da haɗin kai da haɗin gwiwar jama’a.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *