fbpx
Sunday, September 19
Shadow

An kama mutane biyu a matsayin masu karba haraji na bogi a Jihar Benuwe

Hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Benuwe (BIRS), ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da damfara.

Wadanda ake zargin guda biyu, Angulu Abdu da Chiahemba Ikyo, dukkansu an kama su ne a Ipav, karamar hukumar Gboko, a tashar jirgin sama, hanyar Gboko/Ihugh.

Su biyun sun saka alamar ma’aikatan haraji akan hanyar inda suke amshe kudaden mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Tuni dai aka mika su ga ‘yan sanda don ci gaba da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *