fbpx
Saturday, October 16
Shadow

An kama mutane uku da ake zargi da damfara ta intanet a Abuja (hotuna)

Jami’an hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da damfara ta intanet a yankin Kuje da Gwagwalada na Abuja.

Wadanda ake zargin sune Adejobi Riliwan, Igwe Dominic da Sunday David. An damke su ne a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, a wani samame, biyo bayan sahihan bayanan sirri da Hukumar ta samu akan zargin su da hannu a cikin damfara ta yanar gizo.

Abubuwan da aka kwato sun hada da kwamfutoci da wayoyin hannu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *