fbpx
Monday, September 27
Shadow

An kama mutumin da ake zargi da dukan wani dan achaba har lahira a Jihar Ogun

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke Michael Salako mai shekaru 40 a duniya bisa zargin lakadawa wani dan achaba da aka fi sani da Okada direba har lahira a yankin Lafenwa da ke Abeokuta.

Wata sanarwa da DSP Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ya fitar ta ce an cafke wanda ake zargin ne bayan wani kiran gaggawa da hedikwatar sashen Dpo Lafenwa ta samu, da misalin karfe 12 na rana, cewa an yi wa wani dan achaba duka har lahira a kan titin Sanni, Lafenwa Abeokuta.

Da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin, ya yi ikirarin cewa ya san marigayin a cikin unguwarsu ya sanar da ‘yan sanda cewa ya nemi marigayin ya kai shi wani wuri da babur dinsa a ranar da ta gabata kuma marigayin ya ki.

Ya ci gaba da cewa lokacin da ya gan shi a wannan karon, ya tambayi margayin kan dalilansa na kin daukar sa a ranar da ta gabata kuma hakan ya haifar da fada tsakanin su. Yayin da ake ci gaba da fafatawar, marigayin ya yanke jiki ya fadi kuma nan take ya mutu.

Abimbola ya ce an ajiye gawar wanda aka bayyana da sunan Abudu a dakin ajiye gawa don yin bincike.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda, CP Edward Awolowo Ajogun, ya ba da umurnin a gaggauta mika wanda ake zargin zuwa sashin bincike kisan kai da manyan laifuka na jihar da hukumar leken asiri domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da shi a gaban kuliya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *