fbpx
Sunday, September 19
Shadow

An kama mutumin da ake zargi da satar wayoyin wutar lantarki a Jihar Adamawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wani mutum mai suna Haruna Muhammed, bisa zarginsa da lalata da satar wayoyin lantarki masu sulke.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Suleiman Nguroje, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce Muhammed yana daya daga cikin sanannun wadanda ake zargi da yin barna da satar igiyoyin wutar lantarki da suka hada garin Mubi da kauyukan da ke makwabtaka da shi.

Ya kara da cewa, “wanda ake zargin, Haruna Muhammed, dan shekara 29, mazaunin Angwan Kara, karamar hukumar Mubi ta Kudu an kama shi a maboyarsa da ke tare da Mugulvu a bayan makabarta yayin da yake jiran wadanda ke tare da shi.

Rundunar ta ce Kwamishinan ‘yan sanda, CP Aliyu Adamu Alhaji, wanda ya yaba wa jami’in‘ yan sanda na yankin, Mubi kan yadda suka hana wadannan masu aikata miyagun laifuka su kubuta daga kamun, hakazalika ya yi kira ga sauran jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai kan lokaci dangane da kowane mutum ko gungun mutane masu hali mara kyau a kewayen unguwarsu ga ‘yan sanda.

Shugaban ‘yan sandan ya kuma bayar da umurnin a gudanar da bincike a kan lamarin sannan ya ba da tabbacin cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *