fbpx
Sunday, September 19
Shadow

An kama tsohon soja da wani tare da tabar wiwi mai darajar N7.5m yayin da sojoji suka fatattaki kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi a Kaduna

Dakarun Operation SAFE HAVEN (OPSH) a ranar Talata, 14 ga watan Satumba, sun fatattaki wata kungiyar miyagun kwayoyi tare da gano katon 248 da ake zargi da wiwi da aka kiyasta sun kai kimanin naira miliyan 7.5 a Kaduna.

Jami’in watsa labarai na rundunar, Manjo Ishaku Takwa, ya ce an boye sinadarin ne a cikin mota Toyota Camry mai lamba Lagos, KJA 150 EG.

Takwa ya bayyana cewa, daga cikin wadanda ake zargin sun hada da, tsohon Kofur Essien Jumma’a, wani soja mai ritaya mai shekaru 60 da Ibrahim Ali, mai shekaru 50, sojoji sun kama su a lokacin da suke tsaida da bincike a kan hanyar Manchok-Jos a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.

Wadanda ake zargin sun yi iƙirarin cewa an ba su kwangilar isar da kayan ne zuwa Yola, jihar Adamawa daga jihar Ondo.

Wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato an mika su ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, rundunar jihar Filato don ci gaba da bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *