fbpx
Thursday, July 29
Shadow

An kama wani da ake zargi da yin garkuwa da mutane a yayin da yake gyara mota da suke amfani da ita a wani gareji dake Jihar Delta

Jami’an ‘yan sanda na jihar Delta sun cafke daya daga cikin wadanda ake zargi da yin garkuwa da wani saurayi a karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar.

Mai rikon mukamin kakakin rundunar, DSP Bright Edafe, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ya ce wanda ake zargin, Godspower Omosomvofa tare da mambobin kungiyar sa sun sace wani Tayo Badamosi a kan hanyar Ughelli a watan jiya.

Edafe ya ce, ‘yan sanda sun binciki wanda ake zargin zuwa wani gareji a Warri inda ya je gyaran motar da aka yi amfani da ita.

An kama wanda ake zargin cikin gaggawa tare da motar baka kirar Toyota Corolla mai lamba. YEN 346 LA da ‘yan bindigar suka yi amfani da ita wajen aikata mugayen laifuka.

Wanda aka sace din, ya gane wadanda ake zargin da kuma motar ta su. Ana ci gaba da farautar sauran mambobin kungiyar kafin a gurfanar da su a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *