fbpx
Sunday, September 19
Shadow

An kama wani Malami bisa zargin yadawa yara 14 cutar kanjamau a Jihar Neja

Rundunar yan sanda ta kama Usman Galadima wanda malami ne a makarantar firamare dake karabonde, karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja, kan zargin lalata yara 14 tare da yada masu cutar kanjamau.

Bayan kama shi da kuma binciken ‘yan sandan jihar, gwamnatin jihar Neja ta kuma kafa kwamitin da zai binciki zargin da aka yi masa.

Kwamitin na karkashin jagorancin Kwamishinan Ilimi ta jihar, Hajiya Hanatu Jibrin Salihu.

Sauran membobin kwamitin sun hada da Daraktan Hukumar Kare Hakkin Yara, Kwamishinan Harkokin Mata na jihar, SUBEB, Board da sauransu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *