fbpx
Monday, May 10
Shadow

An kama wani matsafi da kai da hannuwan wani da ya kashe, yace Sunan wanda ya kashe din Muhammad

Gazetteng: Matsafin da aka kama

Jami’an tsaro a jihar Kwara sun kama wani matsafi da kan mutum da kuma hannuwa.

 

Wanda aka kama din, Kehinde Moses ya bayyana cewa sassan jikin na wani ne me suna Muhammad da aka kashe dan yin tsafi.

 

An kamashi ne a karamar hukumar Irepodun dake jihar. Kakakin ‘yansandan jihar, Ajayo Okasanmi ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Yace abokin laifin matsafin ya tsere yayin da suka tsayar da motarsu akan hanya. An yi kamenne jiya Litinin, 3 ga watan Mayu, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *